Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.

  2. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.

  3. ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.

  4. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.

  5. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,

  6. yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.

  7. Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.

  8. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,

  9. kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.

  10. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.

  11. Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya.

  12. Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?

  13. Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce.

  14. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.

  15. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.

  16. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,

  17. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

  18. Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba.

  19. Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.

  20. Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba.

  21. Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba?

  22. Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.

  23. Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.

  24. In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne.

  25. Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka.