Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da War

639 ayoyi · 45 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.

  2. Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.

  3. Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya

  4. saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

  5. Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.

  6. Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.

  7. Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,

  8. sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.

  9. Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.

  10. Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.

  11. Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

  13. Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.

  14. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.

  15. Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.

  16. A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela

  17. Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.

  18. Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.

  19. Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.

  20. Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu.

  21. Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.

  22. waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa.

  23. Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.

  24. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

  25. shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.