Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da War: Of extermination

87 ayoyi · 45 fannoni

Ayoyi game da Of extermination

Tace bisa littafi
  1. Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  2. A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi.

  3. Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima.

  4. Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu.

  5. Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi,

  6. suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko.

  7. Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani.

  8. Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi.

  9. Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai?

  10. Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji.

  11. Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji,

  12. sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa.

  13. A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba.

  14. Muka hallaka su ƙaƙaf, kamar yadda muka yi wa Sihon sarkin Heshbon, muka hallaka kowace birni, maza, mata da yara.

  15. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi.

  16. Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku.

  17. Haka za ku yi da dukan biranen da suke nesa da ku, waɗanda kuma ba na al’ummai da suke kusa ba.

  18. Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.

  19. Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku.

  20. In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

  21. Suka miƙa wa Ubangiji birnin, suka hallaka kowane abu mai ran da yake cikin birnin da takobi, maza da mata, yara da tsofaffi, shanu, tumaki da jakuna.

  22. Sa’an nan suka ƙona birnin tare da dukan abin da yake ciki tatas, amma suka sa azurfa da zinariya da kayan tagulla da na ƙarfe a cikin ma’aji na haikalin Ubangiji.

  23. Da Isra’ilawa suka gama kashe duk mutanen Ai a filaye da kuma a cikin jeji inda suka fafare su, kuma da aka karkashe kowane mutumin Ai da takobi sai dukan Isra’ilawa suka koma Ai suka karkashe duk waɗanda suke cikinsa.

  24. A ranan nan, dukan mutanen Ai da aka kashe, mutum dubu goma sha biyu ne maza da mata.

  25. Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.