Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da War: Wisdom required in

9 ayoyi · 45 fannoni

Ayoyi game da Wisdom required in

  1. Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.

  2. don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.

  3. An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.

  4. A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan.

  5. Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.

  6. Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa ta fi ihun mai mulkin wawaye.

  7. Hikima ta fi kayan yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa.

  8. “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin?

  9. In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.