Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da War

639 ayoyi · 45 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,

  2. sai ya tara wa kansa ’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba.

  3. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.

  4. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

  5. “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu.

  6. Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.

  7. Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”

  8. Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha.

  9. Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.

  10. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa.

  11. Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.”

  12. Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”

  13. Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”

  14. Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”

  15. Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila sun warwatsu a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyaya, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowanne yă tafi gida cikin salama.’ ”

  16. Da shekara ta kewaye, mayaƙan Aram suka yi gāba da Yowash suka kai hari wa Yahuda da Urushalima suka kuma kashe dukan shugabannin mutane, suka aika da dukan ganima zuwa ga sarkinsu a Damaskus.

  17. Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash.

  18. A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.

  19. Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.

  20. sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”

  21. Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.

  22. Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.

  23. Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.

  24. Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.

  25. Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.