Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle

465 ayoyi · 94 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”

  2. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  3. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  4. Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.

  5. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;

  6. Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.

  7. Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci.

  8. “Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.

  9. Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba.

  10. Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina.

  11. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

  12. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.

  13. Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal,

  14. amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya

  15. Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba.

  16. Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule,

  17. inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.

  18. wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.

  19. Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”

  20. Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.

  21. An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.

  22. Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,

  23. wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.

  24. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.

  25. Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.