Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle: Materials for, voluntarily offered

39 ayoyi · 94 fannoni

Ayoyi game da Materials for, voluntarily offered

  1. Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.

  3. “Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla,

  4. shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya,

  5. fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya,

  6. mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,

  7. da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  8. “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu.

  9. Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.

  10. Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;

  11. shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya;

  12. fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya

  13. da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;

  14. duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  15. “Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta,

  16. “wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;

  17. akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;

  18. tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;

  19. wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;

  20. bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;

  21. bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.

  22. Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;

  23. turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;

  24. saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don ’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”

  25. Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa,