Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle: Sanctified

10 ayoyi · 94 fannoni

Ayoyi game da Sanctified

  1. a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.

  2. “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.

  3. Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.

  4. Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.

  5. “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.

  6. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.

  7. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.

  8. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”

  9. Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.

  10. Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.