Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle: Supported by bars of shittim wood resting in rings of gold

7 ayoyi · 94 fannoni

Ayoyi game da Supported by bars of shittim wood resting in rings of gold

  1. “Ka kuma yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya na tabanakul,

  2. biyar domin katakai wancan gefe, biyar kuma domin na gefe wajen yamma, can ƙarshen tabanakul.

  3. Sandan da yake tsakiyar katakan, zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.

  4. Ka dalaye dukan katakan da zinariya, ka kuma yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Ka kuma dalaye sandunan da zinariya.

  5. Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul,

  6. biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul.

  7. Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan.