Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle: Of the Church

6 ayoyi · 94 fannoni

Ayoyi game da Of the Church

  1. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  2. Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci.

  3. “Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.

  4. wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.

  5. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta.

  6. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu.