Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle: Offerings brought to

8 ayoyi · 94 fannoni

Ayoyi game da Offerings brought to

  1. a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.

  2. Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji.

  3. Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;

  4. a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.

  5. sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.

  6. A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu.

  7. Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama.

  8. Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku.