Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strife

158 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

  2. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

  3. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  4. Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

  5. Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

  6. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.

  7. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.

  8. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

  9. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.

  10. Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.

  11. Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka.

  12. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.

  13. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

  14. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

  15. Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.

  16. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.

  17. Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.

  18. Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

  19. Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

  20. kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?

  21. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.

  22. Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.

  23. In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

  24. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.

  25. Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;