Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strife

158 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

  2. In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.

  3. In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.

  4. Sai ya aiki ’yan saƙo, su yi gaba. Su kuwa, suka shiga cikin wani ƙauyen Samariyawa, don su shirya masa abubuwa.

  5. Amma mutanen ƙauyen ba su karɓe shi ba, don yana kan hanyar zuwa Urushalima ne.

  6. Da almajiransa, Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka yi tambaya suka ce, “Ubangiji, kana so mu kira wuta ta sauka daga sama ta hallaka su?”

  7. Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su.

  8. Sai shi da almajiransa suka tafi wani ƙauye.

  9. Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.

  10. Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne.

  11. Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun.

  12. Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”

  13. Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.

  14. Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”

  15. Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.

  16. Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.

  17. Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,

  18. Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu.

  19. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.

  20. Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.

  21. Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.

  22. Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.

  23. Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.

  24. Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.

  25. Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.