Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strife: General references

124 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne.

  2. Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”

  3. Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?

  4. Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi.

  5. Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.

  6. Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.

  7. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.

  8. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,

  9. wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,

  10. wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

  11. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  12. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

  13. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

  14. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  15. Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

  16. Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

  17. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.

  18. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.

  19. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

  20. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.

  21. Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.

  22. Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka.

  23. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.

  24. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

  25. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.