Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strife

158 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.

  2. Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.

  3. ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku.

  4. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”

  5. Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne?

  6. ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai.

  7. Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?

  8. Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

  9. To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba.

  10. Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

  11. In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka?

  12. Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan.

  13. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan!

  14. Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya!

  15. Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba?

  16. Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi?

  17. Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku?

  18. In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.

  19. Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce.

  20. Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.

  21. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.

  22. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.

  23. Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.

  24. In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.

  25. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;