Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.

  2. Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.

  3. Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.

  4. Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

  5. A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

  6. mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,

  7. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

  8. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,

  9. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  10. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  11. Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.

  12. Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila.

  13. Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.

  14. Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi.

  15. Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.

  16. “Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.

  17. Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?

  18. Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.

  19. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”

  20. Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.

  21. A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.

  22. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi.

  23. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

  24. Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

  25. Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”