Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables

452 ayoyi · 74 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

  2. “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.

  3. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.

  4. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.

  5. “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.

  6. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’

  7. Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.

  8. “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.

  9. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

  10. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  11. “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

  12. “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.

  13. Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.

  14. Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.

  15. Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.

  16. “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci?

  17. Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka.

  18. Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.

  19. Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’

  20. Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.

  21. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.

  22. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  23. “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.

  24. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.

  25. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.