Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: King going to war

3 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da King going to war

  1. “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin?

  2. In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.

  3. Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.