Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: Good Shepherd

6 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Good Shepherd

  1. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

  2. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.

  3. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.

  4. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.

  5. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”

  6. Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.