Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: Importunate widow

8 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Importunate widow

  1. Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa.

  2. Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba.

  3. A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.’

  4. “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba,

  5. amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”

  6. Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce.

  7. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?

  8. Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”