- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: Tares
Ayoyi game da Tares
Yesu ya ba su wani misali. “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa.
Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa.
Sa’ad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.
“Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’
“Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’ “Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’
“Ya amsa ya ce, ‘A’a, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar.
Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”
Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”
Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum.
Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,
abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.
“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.
Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.
Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.
Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”