Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: The boiling pot
Ayoyi game da The boiling pot
Ka faɗa wa wannan gidan ’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta ka kuma zuba ruwa a cikinta.
Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.