Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables: Importunate friend

5 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Importunate friend

  1. Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku,

  2. domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’

  3. Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’

  4. Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.

  5. “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.