Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parables

452 ayoyi · 74 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”

  2. “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.

  3. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.

  4. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.

  5. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’

  6. Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

  7. “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’

  8. “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’

  9. “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin.

  10. Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.

  11. “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni.

  12. Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’

  13. Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.

  14. “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”

  15. “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.

  16. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

  17. “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.

  18. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’

  19. Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka.

  20. Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’

  21. “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

  22. “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’

  23. “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.

  24. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.

  25. Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.