Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountains

136 ayoyi · 82 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,

  2. Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.

  3. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.

  4. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

  5. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.

  6. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

  7. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.

  8. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.

  9. Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu.

  10. Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.

  11. Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.

  12. shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.

  13. duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.

  14. ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

  15. Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.

  16. Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.

  17. Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.

  18. ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

  19. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,

  20. Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai.

  21. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki ya yi kamar garken awaki da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad.

  22. Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, zan je dutsen mur da kuma tudun turare.

  23. Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, zo tare da ni daga Lebanon. Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, daga ramin zaki da kuma dutsen da damisoshi suke zama.

  24. Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar ’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.

  25. A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.