Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trust

109 ayoyi · 66 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka.

  2. Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.

  4. Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji; na ce, “Kai ne Allahna.”

  5. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

  6. A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.

  7. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  8. Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

  9. Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

  10. Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

  11. Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

  12. Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.

  13. Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

  14. Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara;

  15. waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?

  16. “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

  17. Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin.

  18. ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?

  19. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela

  20. Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,

  21. Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

  22. gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.

  23. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.

  24. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

  25. Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.