Skip to content

Pharaoh

5 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Pharaoh

  1. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.

  2. Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai; mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani. Yaya za ka ce wa Fir’auna, “Ni ɗaya ne cikin masu hikima, almajirin sarakuna na dā can”?

  3. waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.

  4. Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya.

  5. Yanzu duba, kana dogara ga Masar, wannan ɗan tsinken kyauron dogarawa, wanda zai soki hannun mutum yă kuma ji masa rauni in ya dangana a kansa! Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara da shi.