Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tabernacle

465 ayoyi · 94 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  2. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  3. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  4. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  5. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.

  6. A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.

  7. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  8. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  9. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  10. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  11. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.

  12. Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.

  13. Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.

  14. Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.

  15. Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi.

  16. Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

  17. “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada,

  18. A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta.

  19. Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta.

  20. Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada.

  21. A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida.

  22. Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran.

  23. Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi.

  24. A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

  25. Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”