Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Repentance

343 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,

  2. “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,

  3. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  4. Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

  5. Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa.

  6. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

  7. “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?

  8. Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.

  9. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  10. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  11. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  12. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  13. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  14. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  15. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  16. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  17. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;

  18. amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

  19. Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.

  20. Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.

  21. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

  22. Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.

  23. Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.

  24. Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah.

  25. Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ya kira ku a wannan rana don ku yi kuka ku yi ihu, don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.