Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Repentance

343 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.

  2. Ku ji ku kuma saurara, kada ku yi girman kai, gama Ubangiji ya yi magana.

  3. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.

  4. Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.

  5. in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata.

  6. in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.

  7. “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’

  8. Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu.

  9. Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin.

  10. Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata.

  11. Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.

  12. Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne.

  13. Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’

  14. Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba.

  15. Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.”

  16. Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.”

  17. ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku.

  18. “A kwanakin nan, a wannan lokaci,” in ji Ubangiji, “mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu.

  19. Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su kuma juya fuskokinsu wajenta. Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji a madawwamin alkawari da ba za a manta da shi ba.

  20. Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa.

  21. “Za su dawo gare ta su kawar da dukan mugayen siffofi da gumaka masu banƙyama.

  22. Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama.

  23. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

  24. “Saboda haka ɗan mutum, ka tattara kayanka don zuwa zaman bauta, ka tashi da rana suna gani ka ƙaura a inda kake zuwa wani wuri. Mai yiwuwa za su gane, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.

  25. “Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama!