Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Repentance: Condition of God's favor

4 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da Condition of God's favor

  1. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,

  2. waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,

  3. zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.

  4. in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.