Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Repentance: Not led to by the judgments of God
Ayoyi game da Not led to by the judgments of God
Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.
Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.