Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Repentance: Exhortation to

21 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da Exhortation to

  1. Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.

  2. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  3. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  4. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  5. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  6. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  7. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  8. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  9. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  10. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;

  11. amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

  12. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri.

  13. In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku,

  14. Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata.

  15. Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku. Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!

  16. Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu.

  17. Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”

  18. Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;

  19. kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”

  20. Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

  21. yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”