Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rain

116 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;

  2. ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma.

  3. Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace.

  4. Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.

  5. Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

  6. Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu.

  7. “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina,

  8. zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.

  9. Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.

  10. Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.

  11. Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

  12. sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.

  13. don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.

  14. Ubangiji zai juye ruwan saman ƙasarku yă zama ƙura da gari; zai sauko daga gizagizai har sai kun hallaka.

  15. Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.

  16. Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.

  17. Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.

  18. Da Filistiyawa suka ji labari an shafe Dawuda sarki a bisa Isra’ila, sai suka haura da ƙarfi sosai don su nema shi, amma Dawuda ya ji labarin sai ya gangara zuwa mafaka.

  19. To, fa, Filistiyawa suka zo suka baje ko’ina a cikin Kwarin Refayim;

  20. saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”

  21. Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.

  22. Filistiyawa suka bar gumakansu a can, Dawuda da mutanensa kuwa suka kwashe su.

  23. yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’

  24. “Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su,

  25. ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.