Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rain: Promised in due season to the obedient
Ayoyi game da Promised in due season to the obedient
zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.
sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.
Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.