Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rain: Contingent upon obedience
Ayoyi game da Contingent upon obedience
“ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina,
zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.
Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,
sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.