Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rain: The plague of, upon Egypt

7 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da The plague of, upon Egypt

  1. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.”

  2. Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;

  3. ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma.

  4. Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace.

  5. Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.

  6. Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

  7. Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu.