Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.

  2. Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.”

  3. Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila.

  4. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce.

  5. sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa.

  6. sai ɗaukakar Ubangiji ta sauka a kan Dutsen Sinai, kwana shida girgije ya rufe dutsen, a rana ta bakwai, sai Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen.

  7. Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.

  8. Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

  9. “Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

  10. Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa.

  11. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.

  12. ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu,

  13. Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.

  14. Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,

  15. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,

  16. Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

  17. Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.”

  18. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  19. “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.

  20. Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.

  21. Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.

  22. sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.

  23. Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.

  24. Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”

  25. Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba.