Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Persecution

270 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.

  2. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

  3. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.

  4. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.

  5. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.

  6. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.

  7. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.

  8. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.

  9. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.

  10. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.

  11. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata

  13. Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.

  14. Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.

  15. Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.

  16. Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.

  17. Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.

  18. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.

  19. Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;

  20. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  21. Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;

  22. sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.

  23. Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.

  24. Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.

  25. Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.