Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Persecution: Of Jesus

152 ayoyi · 61 fannoni

Ayoyi game da Of Jesus

Tace bisa littafi
  1. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

  2. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?

  3. Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.

  4. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”

  5. Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

  6. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,

  7. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?

  8. Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.

  9. Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.

  10. Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,

  11. “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.”

  12. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.

  13. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

  14. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.

  15. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.

  16. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.

  17. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.

  18. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.

  19. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.

  20. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.

  21. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.

  22. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata

  24. Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.

  25. Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.