Skip to content

Iconium

6 verses

37.8800, 32.4900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Iconium

  1. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.

  2. A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.

  3. Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu.

  4. Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,

  5. ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.

  6. tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu.