Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring

170 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari?

  2. Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.

  3. Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa;

  4. Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni.

  5. Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.”

  6. Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?

  7. Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,

  8. har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?

  9. “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.

  10. Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?

  11. Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”

  12. Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

  13. Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.

  14. Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.

  15. Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.

  16. Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.

  17. Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.

  18. Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.

  19. Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya

  20. saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

  21. Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.

  22. Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.

  23. Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.

  24. Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,

  25. da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?