Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring

170 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku.

  2. Kun kuma sa Ubangiji ya yi fushi a Tabera, a Massa da kuma a Kibrot Hatta’awa.

  3. Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza.

  4. Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.”

  5. Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.

  6. Ayuba ya ce,

  7. “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’

  8. Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.

  9. Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta.

  10. Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni.

  11. Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki.

  12. Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa.

  13. Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,

  14. gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba.

  15. “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?

  16. Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu?

  17. Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama

  18. tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,

  19. da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.

  20. Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.

  21. A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta.

  22. Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.

  23. Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.

  24. “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai

  25. ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,