Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring: Punishment of

8 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Punishment of

  1. Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin.

  2. “Har yaushe wannan muguwar al’umma za tă yi gunaguni a kaina? Na ji koke-koken waɗannan Isra’ilawa masu gunaguni.

  3. Saboda haka ka gaya musu cewa, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji, zan yi muku daidai da abin da na ji kuke faɗa.

  4. A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.

  5. “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki.

  6. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”

  7. Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.

  8. Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,