Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring: Against God

70 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Against God

Tace bisa littafi
  1. Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?

  2. Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.”

  3. Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”

  4. “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  5. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  6. “Har yaushe wannan muguwar al’umma za tă yi gunaguni a kaina? Na ji koke-koken waɗannan Isra’ilawa masu gunaguni.

  7. Saboda haka ka gaya musu cewa, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji, zan yi muku daidai da abin da na ji kuke faɗa.

  8. A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.

  9. Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

  10. Amma game da ’ya’yanku da kuka ce za a kwashe ganima, zan kawo su cikin ƙasar, su ji daɗin ƙasar wadda kuka ƙi.

  11. Amma ku, jikunanku za su fāɗi a wannan hamada.

  12. ’Ya’yanku za su zama makiyaya a nan, shekaru arba’in suna shan wahala domin rashin amincinku, har sai mutum na ƙarshe a cikinku ya kwanta a hamada.

  13. Shekaru arba’in, shekara ɗaya a madadi kwana ɗaya cikin kwanakin arba’in da kuka ɗauka kuka leƙi asirin ƙasa, za ku sha wahala saboda zunubanku, ku kuma san abin da ake nufi da sa ni in yi gāba da ku.’

  14. Ni, Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata waɗannan abubuwa a kan dukan muguwar jama’an nan da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su sadu da ƙarshensu a wannan hamada; a nan za su mutu.”

  15. Saboda haka mutanen da Musa ya aika, su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,

  16. waɗannan mutanen da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta buge su, suka kuwa mutu a gaban Ubangiji.

  17. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”

  18. Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

  19. Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?

  20. Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,

  21. har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?

  22. “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.

  23. Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?

  24. Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”

  25. Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;