Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring: Guilt of encouraging others in

5 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Guilt of encouraging others in

  1. Amma sauran mutanen da suka je tare da shi, suka ce, “Ba za mu iya kara da mutanen nan ba; sun fi mu ƙarfi.”

  2. Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.

  3. Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”

  4. Saboda haka mutanen da Musa ya aika, su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,

  5. waɗannan mutanen da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta buge su, suka kuwa mutu a gaban Ubangiji.