Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murmuring

170 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.

  2. Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.

  3. Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?

  4. An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.

  5. Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.

  6. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  7. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  8. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  9. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  10. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  11. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.

  12. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!

  13. Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.

  14. Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,

  15. na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.

  16. Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.

  17. Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.

  18. Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?

  19. Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”

  20. Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,

  21. Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.

  22. Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,

  23. Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”

  24. Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”

  25. Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.