Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sama’ila 19:37kusan 1023 K.H.

    Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”

  2. 2 Sama’ila 19:38kusan 1023 K.H.

    Sarki ya ce, “Kimham zai ƙetare tare da ni, zan kuwa yi masa abin da ya gamshe ka. Kuma duk abin da kake bukata a wurina, zan yi maka.”

  3. 2 Sama’ila 19:39kusan 1023 K.H.

    Saboda haka dukan mutane suka ƙetare Urdun, sa’an nan kuma sarki ma ya ƙetare. Sarki ya yi wa Barzillai sumba ya albarkace shi, sa’an nan Barzillai ya koma gidansa.

  4. 2 Sama’ila 19:40kusan 1023 K.H.

    Sa’ad da sarki ya ƙetare zuwa Gilgal, Kimham ma ya ƙetare tare da shi. Dukan sojojin Yahuda da rabin sojojin Isra’ila suka ƙetare da sarki.

  5. 2 Sama’ila 19:41kusan 1023 K.H.

    Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?”

  6. 2 Sama’ila 19:42kusan 1023 K.H.

    Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?”

  7. 2 Sama’ila 19:43kusan 1023 K.H.

    Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.

  8. 2 Sama’ila 20:1kusan 1022 K.H.

    Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”

  9. 2 Sama’ila 20:2kusan 1022 K.H.

    Saboda haka dukan mutane Isra’ila suka bar Dawuda don su bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka kasance a wurin sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.

  10. 2 Sama’ila 20:3kusan 1022 K.H.

    Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.

  11. 2 Sama’ila 20:4kusan 1022 K.H.

    Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mutanen Yahuda su zo wurina cikin kwana uku, kai kuwa ka kasance a can kai kanka.”

  12. 2 Sama’ila 20:5kusan 1022 K.H.

    Amma da Amasa ya tafi kiran mutanen Yahuda, ya ɗauki lokaci fiye da lokacin da sarki ya ba shi.

  13. 2 Sama’ila 20:6kusan 1022 K.H.

    Dawuda ya ce wa Abishai, “Ina gani Sheba ɗan Bikri zai ba mu wuya fiye da Absalom. Ka ɗauki mutanen maigidanka ka fafare shi, don kada yă sami garuruwa masu katanga yă tsere mana.”

  14. 2 Sama’ila 20:7kusan 1022 K.H.

    Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.

  15. 2 Sama’ila 20:8kusan 1022 K.H.

    Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi.

  16. 2 Sama’ila 20:9kusan 1022 K.H.

    Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba.

  17. 2 Sama’ila 20:10kusan 1022 K.H.

    Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.

  18. 2 Sama’ila 20:11kusan 1022 K.H.

    Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!”

  19. 2 Sama’ila 20:12kusan 1022 K.H.

    Amasa kuwa yana kwance cikin tafkin jininsa a kan hanya, sai mutumin ya ga dukan sojoji suka zo suka tsaya cik a can. Da ya gane cewa duk wanda ya haura zuwa wurin Amasa sai ya tsaya, sai ya ja gawar Amasa daga hanyar ya kai can cikin wani fili ya rufe shi da zane.

  20. 2 Sama’ila 20:13kusan 1022 K.H.

    Bayan an ɗauke Amasa daga hanya, sai dukan mutane suka bi Yowab don fafaran Sheba ɗan Bikri.

  21. 2 Sama’ila 20:14kusan 1022 K.H.

    Sheba ya bi ta dukan kabilan Isra’ila zuwa Abel da kuma ta dukan yankin Beriyawa, waɗanda suka taru suka bi shi.

  22. 2 Sama’ila 20:15kusan 1022 K.H.

    Sai dukan rundunonin da suke tare da Yowab suka zo suka yi wa Sheba kwanton ɓauna a Abel-Bet-Ma’aka. Suka tara ƙasa kewaye da jikin katangar birnin daidai da tsayinta. Sa’an nan waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe katangar.

  23. 2 Sama’ila 20:16kusan 1022 K.H.

    Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.”

  24. 2 Sama’ila 20:17kusan 1022 K.H.

    Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.”

  25. 2 Sama’ila 20:18kusan 1022 K.H.

    Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama.