- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 19:12kusan 1023 K.H.
Ku ’yan’uwana ne, jikina, jinina kuma. To, don me za ku zama na ƙarshe na yarda a dawo da sarki zuwa fada?’
- 2 Sama’ila 19:13kusan 1023 K.H.
Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”
- 2 Sama’ila 19:14kusan 1023 K.H.
Ta haka ya rinjayi zukatan dukan mutane Yahuda, kamar mutum ɗaya. Suka aika da saƙo wurin sarki suka ce, “Ka dawo, kai da dukan mutanenka.”
- 2 Sama’ila 19:15kusan 1023 K.H.
Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun.
- 2 Sama’ila 19:16kusan 1023 K.H.
Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuda don su taryi Sarki Dawuda.
- 2 Sama’ila 19:17kusan 1023 K.H.
Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da ’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake.
- 2 Sama’ila 19:18kusan 1023 K.H.
Suka haye a mashigin don su ƙetaro da iyalin sarki, su kuma yi duk abin da yake so. Sa’ad da Shimeyi ɗan Gera ya haye Urdun, sai ya fāɗi rubda ciki a gaban sarki
- 2 Sama’ila 19:19kusan 1023 K.H.
ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka riƙe laifina a zuciya. Kada ka tuna da laifin da na yi maka ranka yă daɗe, ranan nan da kake gudu daga Urushalima. Kada ka tuna da shi ko kaɗan.
- 2 Sama’ila 19:20kusan 1023 K.H.
Na sani ni bawanka na yi maka laifi. Shi ya sa na zama na farko daga dukan Gidan Yusuf, da mutanen Isra’ila wanda ya fito don yă tarye ka yau, ranka yă daɗe, sarki.”
- 2 Sama’ila 19:21kusan 1023 K.H.
Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”
- 2 Sama’ila 19:22kusan 1023 K.H.
Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?”
- 2 Sama’ila 19:23kusan 1023 K.H.
Saboda haka sarki ya ce wa Shimeyi, “Ba za ka mutu ba.” Sarki kuwa ya yi alkawari har da rantsuwa.
- 2 Sama’ila 19:24kusan 1023 K.H.
Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba.
- 2 Sama’ila 19:25kusan 1023 K.H.
Sa’ad da ya zo daga Urushalima don yă taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba Mefiboshet?”
- 2 Sama’ila 19:26kusan 1023 K.H.
Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.
- 2 Sama’ila 19:27kusan 1023 K.H.
Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau.
- 2 Sama’ila 19:28kusan 1023 K.H.
Duk zuriyar kakana ba su cancanci kome ba sai mutuwa daga ranka yă daɗe, amma ka ba wa bawanka wuri cikin mutanen da suke ci a teburinka. Saboda haka, wanda ’yanci nake da shi da zan yi wani ƙarin roƙo a wurin sarki?”
- 2 Sama’ila 19:29kusan 1023 K.H.
Sarki ya ce masa, “Me ya sa kake zancen nan? Ai, na riga na umarta, da kai, da Ziba ku raba filayen.”
- 2 Sama’ila 19:30kusan 1023 K.H.
Mefiboshet ya ce wa sarki, “Bari yă ɗauki kome, yanzu da ranka yă daɗe, sarki ya dawo gida lafiya.”
- 2 Sama’ila 19:31kusan 1023 K.H.
Barzillai mutumin Gileyad shi ma ya zo daga Rogelim don yă ƙetare Urdun tare da sarki, yă kuma sallame shi daga can.
- 2 Sama’ila 19:32kusan 1023 K.H.
To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne.
- 2 Sama’ila 19:33kusan 1023 K.H.
Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka ƙetaro tare da ni ka zauna tare da ni a Urushalima, zan kuwa tanada maka.”
- 2 Sama’ila 19:34kusan 1023 K.H.
Amma Barzillai ya ce wa sarki, “Shekara nawa ya rage mini har da zan tafi Urushalima da sarki?
- 2 Sama’ila 19:35kusan 1023 K.H.
Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe?
- 2 Sama’ila 19:36kusan 1023 K.H.
Bawanka zai ƙetare Urdun tare da sarki, yă ɗan yi maka rakiya kaɗan. Me ya sa ranka yă daɗe zai ba ni irin wannan lada.