- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 17:24kusan 1023 K.H.
Dawuda kuwa ya tafi Mahanayim. Absalom kuma ya ƙetare Urdun tare da dukan mutanen Isra’ila.
- 2 Sama’ila 17:25kusan 1023 K.H.
Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab.
- 2 Sama’ila 17:26kusan 1023 K.H.
Isra’ilawa da Absalom suka kafa sansani a ƙasar Gileyad.
- 2 Sama’ila 17:27kusan 1023 K.H.
Sa’ad da Dawuda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lo Debar, da Barzillai mutumin Gileyad daga Rogelim
- 2 Sama’ila 17:28kusan 1023 K.H.
suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,
- 2 Sama’ila 17:29kusan 1023 K.H.
da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu wa Dawuda da mutanensa su ci. Gama sun ce, “Mutanen suna jin yunwa, sun kuma gaji, ga ƙishirwa a hamada.”
- 2 Sama’ila 18:1kusan 1023 K.H.
Dawuda ya tattara mutanen da suke tare da shi, ya naɗa musu komandodi na dubu-dubu, da na ɗari-ɗari.
- 2 Sama’ila 18:2kusan 1023 K.H.
Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”
- 2 Sama’ila 18:3kusan 1023 K.H.
Amma mutanen suka ce, “Ba za ka fita ba; gama in ya kasance tilas mu gudu, ba za su kula da mu ba. Ko da rabinmu sun mutu, ba za su damu ba; amma kai kanka ka fi mutum dubu goma namu. Zai fi maka ka zauna a cikin gari, ka dinga aika mana da taimako.”
- 2 Sama’ila 18:4kusan 1023 K.H.
Sarki ya ce, “Zan yi duk abin da ya fi muku kyau.” Saboda haka sarki ya tsaya kusa da bakin ƙofa yayinda dukan mutane suke fitowa a ƙungiyar ɗari-ɗari da ta dubu-dubu.
- 2 Sama’ila 18:5kusan 1023 K.H.
Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni.
- 2 Sama’ila 18:6kusan 1023 K.H.
Rundunonin suka tafi zuwa fili don su yi yaƙi da Isra’ila. Aka kuwa yi yaƙi a kurmin Efraim.
- 2 Sama’ila 18:7kusan 1023 K.H.
A nan ne mutanen Isra’ila suka sha kashi a hannun mutanen Dawuda. Waɗanda suka yi rauni da kuma waɗanda suka mutu a ranar sun yi yawa, mutum dubu ashirin.
- 2 Sama’ila 18:8kusan 1023 K.H.
Yaƙin ya bazu a duk fāɗin ƙauyukan, abin da kurmin ya ci kawai a ranar ya fi yawan abin da aka kashe da takobi.
- 2 Sama’ila 18:9kusan 1023 K.H.
To, Absalom ya haɗu da mutanen Dawuda. Yana hawan dokinsa, kuma yayinda dokin ya kusa kai cikin rassan babban itacen oak, sai kan Absalom ya sarƙafe a kan itacen oak ɗin. Dokin ya wuce da gudu, shi kuwa ya rataye a can yana lilo.
- 2 Sama’ila 18:10kusan 1023 K.H.
Sa’ad da wani daga cikin mutanen ya gan haka, sai ya gaya wa Yowab, “Na ga Absalom yana rataye a itacen oak.”
- 2 Sama’ila 18:11kusan 1023 K.H.
Yowab ya ce wa mutumin da ya ba shi labarin, “Mene! Ka ga shi? Don me ba ka buge shi har ƙasa nan da nan ba? Ai, da na ba ka shekel goma na azurfa da abin ɗamarar jarumi.”
- 2 Sama’ila 18:12kusan 1023 K.H.
Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’
- 2 Sama’ila 18:13kusan 1023 K.H.
Da na yi haka da na sa kaina a halin ƙaƙa-ni-ka-yi, kuma babu abin da zai ɓoyu ga sarki, kai kuwa za ka janye abinka daga gare ni.”
- 2 Sama’ila 18:14kusan 1023 K.H.
Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak.
- 2 Sama’ila 18:15kusan 1023 K.H.
Masu ɗaukan kayan yaƙin Yowab goma kuwa sun kewaye Absalom, suka bubbuge shi suka kashe.
- 2 Sama’ila 18:16kusan 1023 K.H.
Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, sai sojoji suka bar fafaran Isra’ila, gama Yowab ya tsai da su.
- 2 Sama’ila 18:17kusan 1023 K.H.
Suka ɗauki Absalom, suka jefa shi cikin wani babban rami a kurmin, suka kuwa tula tsibin duwatsu a kansa. Ana cikin haka, sai dukan Isra’ilawa suka tsere zuwa gidajensu.
- 2 Sama’ila 18:18kusan 1023 K.H.
A lokacin da Absalom yake da rai, Absalom ya gina wa kansa al’amudin tunawa, a Kwarin Sarki, gama ya yi tunani ya ce, “Ba ni da ɗa namiji wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Sai ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kuwa kira shi Al’amudin Absalom har wa yau.
- 2 Sama’ila 18:19kusan 1023 K.H.
Ahimawaz ɗan Zadok ya ce, “Bari in ruga in kai wa sarki labari cewa Ubangiji ya cece shi daga hannun abokan gābansa.”